[Book] Rashin Sani (Yafi Dare Duhu) Complete Hausa Novel by Rash A. Kardam

Rashin Sani

BOOK INFO

Name Yafi Dare Duhu
Author Rash A. Kardam
Size 245KB
Format TXT
Category Fiction
Modified Date 23/09/2022
Price Free

BOOK DESCRIPTION

Sauke cikakken littafin marubuciya Rash A. Kardam mai suna, "Yafi Dare Duhu" complete hausa novel a text document. Tabbas labarin ya matukar tsaruwa. Za ku ji dadin karatunsa.

BOOK TEASER

Dukawa tayi kasa tare da zare ƴar sillifas ɗin da ke ƙafarta, ɗan karanin gyalenta da ke ƙuugunta ta kuntoshi tare da zura takalmanta a cikin gyalen ta ɗamare shi a ƙuugunta.

Dan zaninta da ya koɗe ta tattare shi, ta gyara tsayuwarta da kyau ta rike makaɗin tayanta da hannu ɗaya. Daya hannu ta rike tayan. 

“Buwun! Buwun!! Buwun!". 

Tayi wani irin ruri tamkar karan tashin babur tare da sanya ma tayarta giya tamkar wacce take tuka mota ta lula kan hanyar rairaiyin jar kasar da ke kauyen. 

Gudu take tamkar sabuwar Mota da tasha tayu masu ƙarfi da kyau. 

Tun daga nesa na hango gungun Yara suna laɓe. Sam Kausar bata lura da su ba don yanda ta kwalo gudu tamkar barewa ke sharara a dokar daji.

“Kausar Dambun ƙwarƙwata, Kausar kazama”.

Suuu taja wani wawan burkin wanda yayi sanadun tashin ƴar ƙaramar ƙura a gurin, wani irin gurnani tafara yi tamkar Damisa da ta shekara ba abinci ta gama ɗibo yunwa. Wani irin juyi tayi tamkar walkiya a sararin samaniya, a sukwane ta yi kwana ta nufi inda ta ji muryan Yaran na tashi.

Gungun yaran na ganin haka kowa ya arci na kare, don sanin halin Kausar ko a gaban wayen inta rike yaro sai yaji a jikinsa.

Gaba ɗaya Yaran sun watse duk ta rasa wa za ta bi. Can ta ƙyallo shugaban tawagarsu Ɗahe da gudu ta bisa.

Ba a binda ke tashi a bayan Kausar sai kura tamkar Dokin da ke sharara gudu a Sahara, ko ince tamkar wace ta samu sabuwar kwalta ɗoɗar ba gargada, ganin Ɗahe zai tsere ma ganinta ta kara kai gami da zama, kafin ta ankaro ya iso ƙofar gidansu ya shiga da gudu.

Kausar na isowa bata tsaya wata wata ba tayi cikin gidan, cikin zafin nama irin na matashitya da ke ji da yaranta tayi wuf tashige ɗakin Iya Mai kosai.

“ke! Ke!! Ke!!! Kausar lafiya ki ka biyo Ɗahe?".

Kausar bata saurare ta ba tayi cikin ɗakin kasan gadon Iya tayi ta  soma janyo Ɗahe da ya shige kasan gado mai rumfa.

Iya da hanzari ta mike ta soma kiciniyar ɗaura zani tana narka manya manya ashar goron da ya ke  cike fam a bakinta shi ya taimaka guri kumfar da ya cika ta ke bakin ya fara rawa kamar mazari an taɓota Iya mai niman ayaraye nanaye bare an taɓota har gida.

“Lalle yau sai kin gane kuren ki, ki zo har gida kuma har cikin ɗaki zaki biyo min Jika, kuma kice zaki dake shi, don tsabar fitsara da rashin kunya yau sai naga mai kwatarki inga Shegen da ya tsaya miki da ƙafafunsa acikin kauyen nan".

Kafin ta isa Ɗahe ya kurma uban kara.

Kausar sai jibgar sata take tamkar ta samu jakinta.

Kafin kace me jini ya ɓalle ta baki ta hanci dai-dai lokacin Iya tashigo, ganin abunda ya faru, ta zare ido ta dunkulo ashar ta narka.

“Jar uban nan lalle yau sai na karairayaki a gidan nan".

Da sauri ta yi gun Kausar ta kai mata wawar damƙa. 

“Wayyo Ummana Iya zata kashe ni ki zo ki cecen".

Da sauri ta harɗe ƙafarta a jikin Iya ta yanda ba zata iya dukanta ba. Iya ta sa hannuda niyar janyo Kausar ta jibgeta, ba-zato-ba-tsammani naji timmm! Iya ta zube a ƙasa. Da mugun gudu Kausar ta fita daga gidan bata tsaya ko ina ba sai inda ta bar tayanta. Da sauri ta ɗauka tasa gudu, ta nufi hanyar gida. “Aushh! Washhh!! Ja'ira shegeyar Yarinya ƴar banza ta yar dani zata ci kwal ubanta yau har gun mai gari zan kaik'aran ƴarsa. Ni abun ya isheni haka yarinya kamar Aljana, sai shegen fitana da bala'i yau ta taro ni buhun barko no da na masifa sai naga gatanta yau". 

Also Download: Motar Kwadayi Complete Hausa Novel by Rash A. Kardam

Da kyar ta miƙe ta ta janyo Ɗahe da ke kwance a kasa, ta ɗaga sa zuciyarta cike da ƙunci. Kausar bata ja burki a ko ina sai ƙofar gidansu da ya sha fenti irin na masu halin kauyen. Da gudu tayi cikin gidan ko sallama babu. Ummi da ta fito daga ɗakin Mai gari da kwano a hannunta da alama anci abinci ne a ciki, ta ga Kausar ta shigo kai ta girgiza. 

“Allah ya shirya ki Kausar bansan yaushe zaki girma ba? Na sha faɗa miki muhimmacin yin sallama da ladan da ake samu amma sam kin ki kula". Washe hakwaranta tayi da suka rine harsunyi kalan ɗaurawa yalo-yalo dasu tsabar datti.

Kausar sam bata son tsabta ko wanka bata sonyi sai Umma tayi dagaske wani sa'in ma kulle ƙofar gida takeyi ta hanata fita har sai ta dirjeta sosai.

Madafi(kitchen) ta nufa ta ɗauko kwanon abincinta ko hannu bata wanke ba ta fara cin abinci.

Umma da ke kallonta ta ce.

“Kausar na sha gaya miki in zaki ci abinci kina wanke hannu ki sabida dattin da ke hannu ko da wasu cututtuka. In har kin wanke zasu fita,kuma zaki kare kanki da kanuwa da ga wasu kwayan cutta da kananun cututtuka da ido ba zai gani ba".

Kausar sai kai loma take tamkar ba da ita ake yi ba.

Umma ta na kallon yarta a zuciyanta tana mata addu'a Allah ya shiryata.

“Kausar baki fa yi addu'a ba, kin kuma san ba kyau. Don duk wanda ke cin abinci ba bissmilla to yana ci ne tare da Shaiɗan. Shaiɗan kuma in yaga bakayi bissmilla ba, sai yana maka kazanta a cikin abinci misali: kamar yana mayar maka dana baki yana jagwal-gwala abinci. Sannan yin bissmilla kafin cin abinci sunnan Annabin mu ne kuma sunna ne mai ƙarfi dan haka ki dage kinji Kausarata". 

Kai Kausar ta gyaɗa mata taci gaba da cin abincinta.

“Banga kin yi bissmillan ba?".

Kausar ta turo ɗan karamin bakinta kamar zatayi kuka don bata son ana yawan mata magana a hankali ta ce.

“Bissmillahi fil auwalihi wa akhirihi".

Murmushi Umma tayi ta miƙe tare da faɗin. 

“In kin gama kiyi wanka ki saka kayan Islamiya ki tafi".

Kai Kausar ta girgiza ta ci gaba da cin abinci.

Tana gamawa ko wanka bata yi ba ta ɗauko kayan Islamiyarta da ya sha datti tasa, tare da zura mutacciyar silifas ɗinta cikin ƙafarta. Sai da ta lelleƙa ta ga ba kowa a tsakar gidan. Ko ta kan jakar Islamiyyan bata bi ba ta rantama a guje ta bar gidan.

Bata zarce ko ina ba sai inda ta saba laɓewa duk lokacin da zata je makaranta. A rayuwan Kausar sam ta tsani makaranta mafi yawanci in an turata Makaranta yawo ta ke wuce wa, sai ta gama gararambanta da wasa kafin ta dawo gida. Tana isa gun yara suka fara sowa sun ga abokiyar wasansu ta iso. Kakkasuwa suka yi kamar yanda suka saba in zasuyi tambo yar gida. Basu jima ba gurin raba kawunan su suka fara fafatawa.

Yau dai wannan wasa ba sa'a don an cinye 'yan gidansu, nan rinto fa ya kacame wanda har ya ƙusa dawo musu faɗa. Kiran sallah magriba ya dawo da Kausar daga rikicin da suke yi. Ga gari ya soma *duhu* da sauri ta ɗibi gudu tayi hanyar gida ko ta kan ƴan rinton tambo bata bi ba don tasan mai zai biyo baya muddin ta ce zata tsaya faɗa. Ko da ta isa Malam baya ƙofar gida sun shiga sallah. Da sanɗa ta shiga ɗakinsu tashiga ta ta samu Umma na sallah sai ta ni mi guri ta zauna.

Umma na idar da sallah tayi azkar ɗinta kafin ta kalli Kausar ta ce.

“Ba za ki yi sallah ba ne? A ina ki ka tsaya har magriba ya same ki a waje?".

Idon Kausar ya yi tsuru-tsuru don bata da amsar tambayar da Ummanta tayi mata.

Sai da Umma ta maimaita mata tambayar.

“Umm da man mun tsaya share makaranta ne sabida gobe in mun zo bitan karatu zamu fara ba sai munyi shara ba".

Umma ta kalleta ba wai ta gama gamsuwa da amsarta ba ne don tasan halin kayanta. 

“To sallah fa ko shima kinyi?".

Kiri kiri Kausar ba kunya ta amsa da. 

“Eh nayi a makaranta bayan da muka gama shara".

Da sauri Umma ta ɗago ta kalleta tana tafa hannu gami da girgi za kai alamar mamaki.

      “Muga kafarki Kausar in har kinyi sallah zan gane".

Dasauri Kausar ta shiga ɓoye ƙafarta don ta san bata da gaskiya.

Umma ta soma niman inda ta ajiye bulalanta.

Also Download: Bazata Complete Hausa Novel by Rash A. Kardam

Da sauri Kausar ta miƙ'e ta nufi waje ta ɗauko buta ta saka ruwa a ciki ta fara alwala ta leƙe taga ko Umma bata ganinta. Ruwa ta sheƙa a kafarta da fuska ta miƙe da zuman shigowa ɗaki tayi sallah Umma ta zaro ido ci kin mamakin ta ke kallonta.

   “Lalle yau na ƙara tabbatar da rashin jinki yanzu alwala ki ke wasa da ita? Kin ɗauka bana kallo ki ne?, Kausar ki ji tsoron Allah! Shin ko kin manta da irin bayanin azabar da Allah ya ke yi wa masu wasa da ibada? Ko kin manta sallah ita ce abuna farko da ranar Al-ƙiyyama za'a fara dubawa a cikin ayyukan bayi. In har sallah ka tayi kyau to sauran aikin ma za'a samu da kyau. Kausar ki mai da hankalinki ki nutsu bana son abun da ki ke yi. Maza ina kallonki ki sake alwala tun kafin in sassaɓa miki yanzun nan".

  Kausar ta sake sa ruwa abuta ta fara alwala mai kyau Umma na tsaye a kanta.

Inna Jummai kishiyar Umma ce ta fito daga ɗaki tana harare-harare tare da yin tsaki ta yi shewa tana watso harara a guri da Umma ta ke tsaye.

  Umma bata tanka mata ba ko ta san da wata halitta ma a gurin bare ta kalli inda ta ke ba.

   Ran Inna Jummai ya kara ɓaci ta yi shewa tare da guɗa. “Ehehehe ayyiriri da ba a san asalin angulu ba ai sai muce daga Misra ta ke. Kuma komai ya ke cikin ɗan tsako shaho ya sani. To mai za'a nuna mana? Dan gulma a ce ke kin fi kowa Addini ko me mtsww!".

  Inna Jummai ta ja dogon tsaki, tana jiran taji ko Umma zata amsa ta mata zagin kare dangi da rashin mutunci. 

   Umma na ganin Kausar ta idar da alwala ta umurce da su shiga ɗaki.

Tana  zaune tana kallon Kausar tana sallah sai dai wasa ya ci ran Kausar dan haka ta ɗau aniyar dora ɗiyarta a kan bi'a mai kyau don Iccenka tun na ɗanye kake lankwasa shi.

   Kausar na sallamewa tayi wub zata mik'e Umma ta ce.

“A'a Kausar baki yi azkar kar ɗin da ake yi bayan sallah ba. Kausar kina wasa da ibada zauna ki yi azkhar ana son mutum in yayi sallama ya fara faɗin Astaghafirulla sau uku. Sai ki faɗi Allahumma anta salam wa minka salam tabarakta ya zaljalalu wal ikram sau uku. Sai kiyisalati wa Annabi salati sau uku. Sai ki faɗi Subhanallahi walhamdu lilahi subhanallahi azim. Daganan sai karanto sauran azkhar din tare da karanta ayatul kursiyyu da kulhuwa da kul'azu bi rabbil falak. Sai Kul a'uzu bi rabbi nas...".

  Kausar ta koma tazauna ta fara karantawa.

   “Yauwa idar in faɗamiki falalar sallah da azabar da ake yi wa mai wasa da ita". Cewar Umman Kausae.

   Kausar tana idar da azkar ta jiyo tana fuskanta Umnanta, ta tankwashe ƙafafunta kamar mai cin abinci.

Umma tayi gyaran murya ta soma da ce wa.

        _“Mai wasa  da Sallah zai haɗu da uƙubobi goma sha huɗu: Uƙubobi Biyar Anan Duniya, uku a lokacin mutuwa, uku a cikin kabari, uku lokacin da zai fita daga kabari. Uk'ubobin da zai haɗu da su tun anan duniya sune:- na farko Za'a cire albarka a cikin rayuwarsa. Na biyu Za'a shafe kamannin salihai daga fuskarsa. Na uku Duk aikin da zai aikata ba za'a ba shi lada ba. Na huɗu Addu’arsa ba zata ɗaukaku ba (ma’ana ba za a karbi addu’arsa ba). Na biyar Bashi da rabo a cikin Addu’o’in bayi nagari. UK'UBOBI DA ZASU SAME SHI A LOKACIN MUTUWARSA SUNE: Na shidda Zai mutu wulakantacce(wan da azaba da fitinar kabari suke jiransa). Na bakwai Zai mutu Yyana mai jin yunwa. Na takwas Zai mutu yana mai jin kishirwa koda za'a shayar da shi da kogunan duniya ba za su raba shi da kishirwa ba. UKUBOBIN DA ZA SU SAME SHI A CIKIN KABARINSA SUNE: Na tara Za'a kuntata kabarinsa har sai hakarkaninsa sun saɓawa juna. Na goma Za'a kunna wuta a kabarinsa yana jujjuyawa a kan garwashin wutar"._ 

   Ummata k'arashe maganan tana mai faɗin. “Ya Allah! Ka bamu ikon bauta maka kuma ka k'ara mana juriya da jajircewa wajen bautarka amin". 

Duk jikin Kausar ya gama yin sanyi da jin wa ƴannan kalaman Ummanta.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post