[Book] Rubutaccen Al'amari Complete by Aysha Ali Garkuwa

Rubutaccen Al'amari

BOOK INFO

Name Rubutaccen Al'amari
Author Aysha Ali Garkuwa
Size 65OKB
Format TXT
Category True Life Story
Modified Date 20/09/2022
Price Free

BOOK DESCRIPTION

Labarin da ya faru da gasken-gaske. Ku suke littafin marubuciya Aysha Ali Garkuwa mai suna, "Rubutaccen Al'amari" complete hausa novel a text document. Za ku iya daukarsa daga wannan shafin yanzu.

BOOK TEASER

Suna iso kan layin uguwar tasu Usman ya dafa kafad'un abokin shi Nura dake jan motar tasu cikin dan fidda ido yace.

"Kai Nuru tsaya a nan ba sai ka shiga cikin gidaba zan sauk'a a nan!."

Kai Nuru ya juyo tare da k'are mishi kallon sai kuma yayi murmushi ganin yadda Usman sarkin surutu ya wani zaro ido cikin murmushin yace.

"Kai Usman ni wallahi Hamma Umar mamaki yake bani ji yadda yake wani tsareka a gida kamar mace! ji yadda kake wani zaro ido dan kasan yanzu yana harabar gidan yana duba marasa lafiyan dake zuwa gunshi.

Shi dai Usman balle marfin motar yayi ya fita yana hararan Nuru tare da cewa.

"Ban za kawai lailamajanun duk ka zama majanuni akan mace sai dare yayi kazo kace in raka ka kakuwa sani sarai Hamma Farouq zai nemeni dan zai bani magani na."

Shi dai Nuru dariya yayi tare da jan motarsa ya tafi.

Shi kuwa Usman cikin sand'a da d'an d'aga k'afa da lek'e-lek'e ya shiga cikin gidan,

gaba d'aya hankalin shi na can gefen wasu yan bukkoki da akayi da ginin zamani sai samansu kuwa da akayiwa rufi da ciyawa suka fita kamar bukkokin rigar Fulani sai fulawowi masu kyau da suka zagaye harabar gidan da haske tako ina cikin bukkokin da sukafi kama dana shak'atawa wani farin matashi ne mai cikar haiba da tsurawa wanda yafi kama da laraba Dr Umar Faruoq kenan shine yake  zaune kan kujerun dake zagaye a bukkokin sai mutane kusan 8 dake zaune daga dukkan alamu sunzo ya duba lafiyar sune gaba d'aya hankalin shi na kansu.

Also Download: Miwasmiti Complete by Aysha Ali Garkuwa

Shiko Usman ganin haka yasa cikin sauri da d'an d'aga k'afa ya zille yayi cikin gidan,

kai tsaye Parlour Nenne ya nufa cikin yana yinsa na fara'a yayi sallama,

tare da shiga cikin Parlour yana ta haki da d'an zare ido.

Nenne ce ta fito daga cikin bedroom cikin sakin fuska tace.

"Usman daga ina haka kaketa zare ido?."

Dariya ya d'an yi tare da zamewa ya zauna gefen Ummul dake ta binshi da ido sai ya Adam da ya Sadik dake zaune a gafe duk sun zubawa Usman ido cikin murmushi Ummul tace.

"Mugun ne ya koroka ko ya Usman?."

Kai ya d'an juya cikin sauk'e ajiyan zuciya yace.

"Tab Nenne  Hamma Umar yazo ya nemeni ko.?"

Cikin sauri da salon tsokana ya Adam yace.

"Ehh yazo k'afa 3 yana neman ka."

Ido ya kuma d'an zarowa yace.

"Toh ni fa ba wani wuri naje ba! kawai na d'an raka abokina Nuru zance gun budurwar sane, kuma yanzu nasan Hamma Umar zaice yawo natafi ban sha maganina ba."

Dariya Nenne tayi cikin kula tace.

"A a baizo bafa Usman."

Shima dariya yayi cikin sauk'e ajiyan zuciya yace.

"Ummul me kika dafa mana me? Dan wallahi yunwa nikeji." 

Ya Sadik ne yace.

"A a saidai ta tashi ta dafa maka ko indomi ne dan miyar ganye tayi kai kuma kasan an hanaka ci."

Fuska ya d'an tsuke cikin badda zancen yace.

"Ummul kawomin zanci na yau kawai bazai min komai ba."

Nenne ce ta kalleshi cikin kula tace.

"A a fa Usman ka kiyaye dokokin Doctors ko dan samun lafiyar ka."

Baki ya kuma turawa yace.

"Wallani ni nagaji da wannan dokokin ace duk wani abu green bazan ciba,

dan Allah Nenne yau kawai kinji ko?."

Ita kam Nenne gaba d'aya take jin tausan Usman a ranta sabida ciwon dake tare dashi gashi yaro matashi .

Shi kuwa Usman cikin dariya ya kalli Ya Adam yace.

"Ya Adam kasan me Nuru yakeyi in munje gun babynshi?."

Murmushi ya Adam yayi tare da cewa.

"Inako zan sani sai ka fad'a min dai."

Ummul ce tayi carab tace.

"Ya Usman me yake yi?."

Hannu yasa ya kamo na Ummul d'in cikin yanayin shi na abin dariya yace.

"Jeki kawo min abinci zan baku labari."

"Toh" tace tare da haura saman d'an steps d'in da zai sadata da kitchen d'in sauri-sauri tasa mishi abincin a pilet sannan ta dawo parlour stol tajawo gaban shi ta ajiye mishi abincin cikin son jin zancen tace.

"Toh ga abin cin bamu labarin."

Murmushi yayi cikin raha ya mik'e tsaye tare da cewa.

"Nenne kina jiko kullum Nuru zaizo yace na rakashi zance amman sam in munje ba abinda yake sai shirme."

Ido ya Adam ya tsura mai cikin gimtse dariyar shi yace.

"Kamar yayafa?."

Dariya ya kuma tare da cewa.

"kuna jiko Nenne kullum in munje muna zuwa k'ofar gidan su  budurwar tashi sai Nuru ya kalle ni cikin in inarsan nan yace min k.. k.. kai Bosho k.. katsaya a cikin motar nan karka fito, ni kuma sai nayi dariya nace toh , in an aika ta fito sai yace ta zauna kan motar , ita kuma sai ta wani d'ale  saman motar ta zauna tana kallon shi."

Ajiyan zuciya tayi tare da cewa.

"Hmmmm Nenne kin san me Ruk'ayyan  take ce masa?."

Su ya Adam kam da ya Sadik tuni sun fara dariya itama Ummul sai dariya take .

Ita ma Nenne murmushi take yi tare da girgiza kai alamar a,a.

Shi kuwa Usman cikin nuna musu abin a zahiri ya jawo hannun Ummul ya ajiyeta kan hannun kujera shi kuma ya matso gaban ta gab da ita ya d'an sa k'afarsa d'aya a gaba d'aya kuma ya maidata baya sannan ya rink'a d'an sunkuyawa yana d'an d'agowa kamar maiyin wazifa sai kuma ya kalli ya Sadik yace.

"Ya Sadik Kunga haka ko?,

wallahi haka Nuru yake tsayuwa a gaban ta kamar mai jin bacci yayi ta layi ita kuma sai tayi ta wani mishi murmushi kamar sokuwa."

Sai ya kuma kalli Nenne yace.

"Nenne kin san me take ce mata kuwa.?"

Cikin dariya tace.

"Me yake ce mata?."

Dariya yayi tare da koikoyar muryar Ruk'ayya budurwar Nurun  yace.

"sai tace ,Nuru ina sonka."

Sai kuma yayi dariya yace.

"Nenne ba tace masa Nuru  ina sonka ba?."

Cikin dariya Ummul tace.

"Ehh".

Shima dariya ya kumayi tare da cewa.

" shi  kuma soko sai ya kalleta murya can k'asa yace.

"Allah ya d'aiyiba."

Sai kuma suka rink'a dariya cikin dariya Usman yace.

"Kijifa Nenne wai Allah d'aiyiba sai kace wad'anda akayiwa haihuwa Allah ko Nuru yana bani dariya shi yasa nake son rakashi zance, kumafa kullum haka suke hirar tasu ,tace  Nuru ina sonka shiko gogan yace, Allah d'aiyiba."

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post