[Book] Rukayya Yar Albarka Complete Hausa Novel by Batul Mamman

Rukayya Yar Albarka

Title: Rukayya Yar Albarka

Author: Batul Mamman

Category: Fiction

Doc Size: 650KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2020

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya "Batul Mamman" mai suna "Rukayya Yar Albarka" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Su uku ne a cikin office din likitan. Sai hadiyar yawu yake yana sake kallon akwatin kudin da yake bude akan table din da ke gabansa. A zuciyarsa kuwa sai nanatawa yake 'yan Nigeria akwai kudin banza. Abinda take so daga gareshi a ganinsa ko a kasarsu zata iya samu. Sai dai kuma bai san dalilinta na tahowa har India ba.

Ya sake kallon kudin.....karbar haihuwa kawai shine ta bashi dalolin nan. Mai cikin ya kalla madam kina da wata lalura ne da tasa zaki iya kudi fiye da abinda asibiti ke bukata? Batare da ta amsa shi ba ta tashi tsaye a gabansa ta daga doguwar rigarta ta zaro wani pillow wanda ta daidaita shi sosai a jikinta kamar cikin gaske.

Dr Gupta ya mike tsaye ba shiri dama ba ciki gareki ba? Duk maganar da turanci yake yinta. Daya matar wadda uwa ce ga mai cikin tace Dr Gupta ka saurareni da kyau magana zamuyi. Ba tun yau ka sanni ba ina zuwa medical check up wurinka. 

Wannan 'yata ce kuma ko sau daya bata taba samun ciki ba tunda take, aurenta shekara takwas kenan. Dr Gupta yayi dan murmushi ai ba matsala tazo inda zaa taimaka mata. Dattijuwar tace babu abinda zaka iya yi mata Dr. A kasar nan kawai taje asibiti ya fi biyar banda na USA, England da Egypt.

Mahaifarta ce take da matsala bazata iya rike ciki ba ko da an daureta. A halin da ake ciki tayiwa mijinta karyar ciki na wata takwas kuma ya yarda saboda bata bari ya ga jikinta ba. 

Ta nuna masa yar tata kalleta da kyau har kiba ta kara don ta nuna alamun ciki kuma kowa a kasarmu da ya kamata ya yarda ya yarda din. yanzu mun taho haihuwa ne wata uku da suka wuce so muna bukatar baby a wurinka. Dama tunda ta fara magana Dr Gupta ya harbo jirginta.

Dr Gupta ya dan share gumi don kuwa bukatarsu babba ce. Yace Madam me ya hana ku nema a can Nigeria, nasan a can zaku sami babies da yawa wanda zasu dace da bukatarku. Dattijuwar tace kaga Dr muna bukatar sirri ne saboda mijinta babban mutum ne. 

Also Download: Al'adun Wasu Complete by Batul Mamman

Idan kuma muka nema a gidan marayu ana cike ciken takardu wanda karshe dai wata rana asiri zai iya tonuwa. Yar tata ta soma masa kuka tana rokonsa. Yace to ba komai amma dole su bashi time ya duba cikin patients din asibitin wadanda suka fito daga kasashen Africa amma bakake don abin ya fi daidai. 

Matar ta ce to Dr mijina fari ne sosai mai tsaho da jiki, idan dan da hali zanso da namiji wanda ka ga iyayensa sun dace da irin yanayin da na kwatanta maka ko kusa da hakan. Dr Gupta yace ba matsala. 

Suka tashi da akwatin kudinsu wanda aka yi masa alkawarin ya zama nashi indai bukatarsu ta biya nan da sati uku zuwa hudu.

Tana shan maganin yana mata dariya saboda yadda take yamutsa fuska. Ta hade rai tana ta hararsa. Gwalo yayi mata ya tashi daga gabanta yana ta dariya. Maryam ta turo baki Hajjaju kin ganshi ko? Hajjaju ta rike masa kunne tace kaga Mukhtar ka kiyayeni. 

Mutum baka da aiki sai tsokana kamar wani yaro. Maryam ta kalle shi tana masa gwalo itama. Yace Hajjaju kinga kina min fada tana dariya ko?  Ta dafe kai ni naga ta kaina. Tunda kuka taho dani kasar nan kun mayar dani mai rabon fada. 

Ta dan ja tsaki abin haushi ma  sai na shiga nayi dumu dumu sai ku gwaleni. Mukhtar da Maryam suka tafa suna dariya. Ta harare su kungani ko....zanyi maganinku ne fitinannun yara kawai. Sake dariyar suka yi har Hajjaju ta tashi zata shiga bandaki sai ta ga Maryam ta dan cije lebe. Da sauri ta dawo ta zauna sannu cikin ne ko? Maryam ta shafa katon cikinta yau babban mutum shurina kawai kake yi tun safe. Hajjaju tayi murmushi ita dai tana kaunar yarinyar nan. Shekara hudu da aure tayi bari yafi biyar sai wannan cikin ne ya zauna da taimakon Allah da dabarun likitoci. 

Sunce mahaifarta ce sam bata da kwarin rike ciki. Watansu na uku kenan a India ana kula da lafiyarta da ta abinda ke cikinta. Hajjaju kanwar babar Mukhtar sannan gidan mijinta kusa yake da gidansu Maryam. Ta dalilinta suka hadu dukkansu maabota barkwanci. 

Maryam na dafe da ciki Mukhtar ma ya dafa yace ke babbar mutum bar ganin na matsu da zuwanki ba'a taba min mata. Haba duk kin hanamu sakat, ko yar soyayyar nan kin wani bake hanya. 

Pillow Hajjaju ta jefa masa yaran nan baku da ta ido. Ni kiyi ki haihu mu koma gida. Haka kawai zaku  bata idanun tsohuwa. Maryam da mijinta suka sake tafawa suna ta dariya. Sannan tace wai bazaka dena kiran dan nan mace ba? Yace anki din, mace zaki haifa min amma kada ta dauko tsiwarki wallahi don nasan wataran za'a doke bakin. 

Hajjaju tace ni dai mai albarka muke fata. Mukhtar yace matar, Maryam ta juyo naam mijin. Ya kalli gefen yatsun hannunsa da na Hajjaju yace kin tuna cewa kin auri dangin cindo ko? Duk wanda ya hada jini da babansu Hajjaju ko ta uwa ko ta uba sai an haifeshi da yatsu shida. Kai tsohon nan jininsa ba dai karfi ba. hajjaju dai rankwashi ta kai masa tace kuma kaga kune kawai masu yanke naku. 

Mu ai duk da abinmu muke rayuwa ta fada tana shafa karamin yatsanta na shida. Mukhtar yace haka kawai na rasa mata? Ai tana haihuwa indai akwai yadda aka cire min nawa haka zaa yanke masa. 

Ya taba wurin da yayi alama ya ce ahhh su sarkin noma Muhammadu Cindo ka bar mana gado har jikoki. Maryam ta rinka dariyar yadda Hajjaju ke binsa tana rankwashi.

Bayan kwana biyu Maryam tana zaune akan kujera a dakinta na asibiti ita kuwa Hajjaju ta dan kwanta akan gadon marasa lafiyan Mukhtar ya shigo da sallama. 

Wani katon akwati yake ja da kyar. Maryam tace mijin ka dawo, sannu da zuwa. Yana murmushi yace yauwa matar. Ya dubi Hajjaju ina wuni mamanmu. Kafin ta amsa yace yanzu sai ki koro min mata ki dare gadon kamar kece mai cikin. Hajjaju ta ce to ka dawo zamu fara ko. 

Ta nuna shi da yatsa ka kiyayeni ni fa babarku ce ba kaka ba. Maryam ta taso ta zauna kusa da ita rabu dashi Hajjajuna. Zamu hada shi da Umma idan muka koma gida. Hajjaju ta dan ture mata hannu ba wani nan. 

Ke da mijin nan naki duk halinku daya. Ni ban ga na zaba ba a cikinku. Suka kalli juna suka tafa suna dariya. Hajjaju a ranta tayi murmushi tana adduar su cigaba da zaman lafiya. Duk halin tsokanarsu mutanen kirki ne duk su biyun ga rikon addini. 

Mukhtar lawyer ne mai zaman kansa wanda ya fara suna a kasar Nigeria saboda kwazo da hazakarsa. Ita kuwa Maryam bana ta gama karatun mass comm, wato aikin jarida. Idan ta koma zata tafi bautar kasa. Sunyi aure tun bayan ta gama secondary school. Suka zauna suna ta hirar baby don sunki yarda a fada musu jinsi bayan scanning. A cewarsu koma meye suna so. Ita Maryam tace namiji tafi so kamar mijinta shima yace mace yake so irinta.

Dr Gupta ya rasa abinda ke masa dadi. Tabbas kudin nan zai ishe shi ya karasa ginin asibitinsa a kauyensu. Matsala daya ya gama binciken bakaken mutanen dake asibitin masu haihuwa su biyar ne. Daya ce yar Nigeria, biyu yan Ghana ne, daya daga Mali sai wata yar Jamaica. Ya rasa da yadda zai bullowa lamarin gaba daya. A wannan yanayin yaga wucewar Mukhtar yana jan akwati. 

Kura masa idanu yayi sosai yana kallonsa. Tabbas ya dace da kwatancen matar nan. Fari, dogo mai jiki duk da ba kiba gareshi sosai ba. Bayansa yabi har dakin da suke. Ya fito ya nemi file dinsu a wurin receptionist. Duk wani bayani na Maryam ya samu dadin dadawa ma sune yan Nigerian. 

Neman likitan da take kula da Maryam yayi cikin hira ya samu dukkan bayanin da yake nema. Sai kuma yayi saa likitar tace ita tana son daukan hutu a sati mai zuwa zata yi tafiya amma sunyi da abokin aikinta zai yi mata nata aikin kafin ta dawo. Dr Gupta yace haba dai ina nan kike neman taimakon wani. 

Kinsan dai shima yan kwanakin nan aiki yayi masa yawa. Ki bani patients dinki ni ba ma sai kinyi min nawa aikin ba idan kika dawo. Ta washe baki da gaske Dr? Yace sosai ma, ai amfanin zaman tare kenan. Cikin kwanaki biyu ya zama likitan Maryam Hassan kuma suka saba sosai da Mukhtar.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post