[Book] Rumana Complete by Maman Khady

Rumana

Title: Rumana

Author: Maman Khady

Category: Love Story

Doc Size: 329KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2019

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya Maman Khady suna "Rumana" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Zaune yake cikin d'aki ya zabga tagumi hawaye kawai ke ziraro mishi daga cikin idanunsa, 'lallai bawa ba abakin komai yake ba wajan ubangijin mu, yanzu nan Haidar d'in shine a haka amatsayin mahaukaci mai hauka tuburan, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wannan wace irin k'addarace wadda ta tsalleke duk shekarun da aka baro baya sai yanzu da Haidar ya zama cikakken mutun saurayi mai hankali, lokacin da yake murna kwai d'ayan da Allah ya bashi ya rayu zai amfana da shi makusantansa da masoyan sama na taya shi murna da samun shi, sai kuma kawai a wayi gari da wannan babbar lalurar? Mai yai zafi haka? menene silar faruwar wannan lalurar? waima waye zai bashi amsar wannan tambayoyin da suke cikin ransa?

Dr.Bashir dake zaune gefen Haidar d'inne yai gyaran murya kamin yace.

"Alhaji wannan kukan da kake yi fa ba mafita bane kuma ba zai zama mafitaba, wannan yaron addu'a yake buk'ata tare da taimako amma gaskiya lamarin akwai daure kai musamman da Dr. is'hak kemin bayanin irin lalurar tashi, amma dan Allah kabar kukan nan da girmanka da komai.''

Cikin yanayi na tsantsar damuwa yace.

"Dr. barni kawai nayi kukana ko Allah zaisa na samu saukin zafin da zuciya ta keyi min rad'ad'i, ina cikin matsanancin tashin hankali Dr wannan yaron shi kad'ai Allah ya bani, na kwallafa raina akan shi gaba d'aya burina na duniya akan shi yake amma kalli yanda ya koma lokaci guda, Ina cikin wani hali Dr ban tab'a tunanin dukiya zatai rashin amfani ba wataran sai a yanzu, ashe dama akwai ranar da kud'in mutun basu amfanar dashi ba akan buk'atar sa?'' Dr.bashir yace.

"Bawai naki ta taka bane alhaji amma dai ya kamata ka duba damuwartaka bata da wani amfani cikin lamarin nan, addu'arka kawai Haidar yake buk'ata.''

''Dr. Kallifa abokan shi sunata aikin su harda wad'anda suka dawo Nigeria tare amma shi yana kwance ba zai amfanin kanshi ba balle ya amfani wani, gashi na rasa wanda zai kularmin dashi tsakani da Allah.'' Dr. Bashir ya mike tsaye tare d cewa. 

''Alhaji zo muje waje na baka wata 'yar shawara.''

Gyarama Haidar d'in lullubin da aka yi masa da bargo yayi kamin ya manna mishi wani zazzafan sumbata akunci sannan yabi bayan Dr d'in yana mai addu'ar Allah yasa shawarar mai bullewa ce. Sai da yasha lemon da aka kawo mishi sannan ya kalli alhajin yace dashi.

''Alhaji ina mahaifiyar yaron nan take?'' Wani yawu alhajin ya had'iye kamin yace.

"Dr bansan inda take ba, amma tabbas nida kaina na koreta kuma wallahi babu abinda tayi min.''  

''Innalillahi Alhaji lafiyarka kuwa? uwar d'an naka zaka kora ka zauna da matan da sai dai kawai suyi ta b'annatar maka da dukiya? Haba alhaji dan Allah, toh gaskiya bari na tashi domin shawarar da zan baka baza tai aiki ba tunda mahaifiyarshi bata gidanka.''

Hannuwanshi yasa ya rufe fuskarshi yana nanata kalmar innalillahi musamman daya tuno ranar da abun ya faru. Wata biyu da fara lalurar Haidar d'in ya tashi da wani irin mummunan kunci daya addabi zuciyar shi, kai tsaye d'akin yaron shi ya nufa nan ya tarar da ita zaune gaban shi tana bashi abinci tana hawaye sabida ganin yanda yake cin rabi yana watsar da rabin tana ta tunanin 'wai Haidar d'inta mai cike da tsafta yau shine a haka.

Also Download:

Ko sallama beyi ba ya shiga tare da fincike Haidar din daga jikinta yana huci yake cewa.

''Ke dallah tashi kibani waje.'' Shine abinda ya fito daga bakin shi. Da mamaki take kallonshi domin tun da take dashi ko kallon banza bai tab'a yi mata ba balle ai maganar tsawa. 

Mikewa tayi tsaye kafin tace dashi. ''Abban Haidar lafiya kuwa?''        

Yarfa mata wani mari yayi kafin yace da ita. ''Ban sani ba, maza ki kwashe kayanki kibar min gida na kafin na wulakantaki wallahi.''

Idanunta waje take kallonshi amma tsabar tashin hankali tama kasa magana sabida fargaba yau ita alhaji ke mari kamar wata 'yarsa. 

"Zaki tashi kosaina tattakaki anan wajan?'' Abun yanzu ya daina bata mamaki sai dai tsoro, Muryarta na rawa tace. 

''Naji zan fita daga rayuwarka gaba d'aya ba gidan kaba ma, amman dan girman Allah ka barni da yarona kaga dai halin da yake ciki babu kuma wanda zai kulamin dashi kamar yadda zai samu agareni, dan Allah kaimin wannan alfarmar kaji Alhaji.''  

Alokacin kallon banza ya bita dashi kafin yace mata. 

''Wallahi koda mutuwa nayi yaro na ba zai koma hannunki ba ballenta ina raye.''

Sautin kukanta ya dinga ji akunnuwan shi kamar alokacin ne take yi masa kukan. Hawayen idanunshi ya share kamin yace a fili.

''Allah ka kawo min mafita.''

Yana cikin wannan halin yana tufka da warwara saiga matarshi ta shigo, Hajiya bilkisu,Idanunshi ya lumshe bayan yai mata kallo guda.  

"Alhaji barka da wannan lokacin?''  

"Yauwa sannunki da gida.'' Cikin yanayi na kwarkwasa da iyayi tace dashi. 

"Alhaji dama cewa nayi ko Haidar yaci abincinsa kuwa?'' Kallonta yayi kamar yana son gano wani abu a fuskarta sannan yace.

"Na bashi tun d'azu harma Dr. yai mishi allurar shi yayi bacci, amma wallahi hajiya kun bani mamaki matuja wallahi, ace wai idan bana gida a cikin ku babu wacce zata iya kula da gudan jinina ko? amma idan anyi magana kuce wai kuna sona ta yaya zan yadda bayan kun bar gudan jinina babu kulawarku? ai shikenan na gode lalurace dai kuma Allah zai iya jarabtar kowa.'' Harara ta bishi da ita bayan ya wuce tana cewa.

''Allah ya kyauta naba wannan katon saurayin abinci a baki balle ai maganar wankin kazantar shi, Allah ya tsare ni dama ka samu nake ta yi maka addu'a Allah yasa ya mutu kowa yama ya huta.''  Fuuu ta tashi tabar falon ta nufi b'angaren ta tana ta faman sababi a cikin zuciyar ta.

Gefen Haidar d'in ya rab'a ya kwanta har lokacin tunani nukurkusar zuciyar shi yake yi wanda har wani zafi-zafi yakeji daga cikin zuciyar shi ya rasa wane kalar ciwo ne wannan da duk wata k'asa da take takama da manyan asibitoci da likitoci ya kai shi amma a banza babu wani cigaba da aka tab'a samu ballantana ace ai an gano abinda yake damunsa ko kuma ace da sauki.    

Zubawa fuskar Haidar d'in ido yayi yana kallon yanda yake ta baccin shi haka kamar mai lafiya amma yana tashi shikenan kuma wannan nutsuwar duk zata kama gabanta.

Wani tuna nine ya fad'o mishi, nan da nan ya mike addu'a ya tofawa Haidar d'in sannan yabar gidan bayan ya kuma duba d'akin ya tabbatar da cewa babu wani abu da zai iya zama makami a gareshi.

Kai tsaye wajan wani abokin shi ya wuce dake can wata unguwar daban, ya koyi sa'a domin yana zuwa ya ganshi ya fito da mota da alama shima fita zai yi. Da dariya ya fito daga cikin motar yana yi tare da cewa.

"Abban Haidar baka kirani ba sai dai kawai na ganka? da ka tarar da bana nan ai da kaji babu dad'i.''

Kai tsaye cikin falon mutumin suka wuce, hira suke yi sosai cike da kaunar juna daga gani abokai ne na gaske. Sai da ya huta kafin yace.

"Wato alhaji aminu akan maganar Haidar ce na dawo gareka domin tabbas na fara lura da abinda kake gaya min game da matana, tabbas sud'in ba masu kaunata bane, toh amma kasan hidima irin wannan tunda har ba kama su nayi dumu-dumu ba bazai yiwu na titsayesuba da zargin.''

"Haka ne alhaji Yusuf shi yasa ai tun farko nace maka kafara bincike tukunna, domin ni wallahi ban yarda dasu ba gaba d'aya dan son duniya ya gama rufe musu ido, nasan zasu iya aikata komai, toh amma yanzu me kake tunanin yi?''

"To nidai a tunanin da nayi cewa nayi inda zan sami wanda zai kular min dashi tsakani da Allah to hankalina zaifi kwanciya tunda kaga yanayin kasuwancina bana zama bane yau bana wannan kasar gobe bana waccan kaga sai hankalina ya tsaya waje d'aya amma wallahi dana tafi hankalina rabuwa biyu yake yi shi yasa kaga bana iya jimawa yanzu duk inda naje zan kokarta na dawo da wuri.'' 

"Eh wannan gaskiya ne, toh amma alhaji aikin ne da wahala wallahi shi yasa duk wanda aka nema sai ya zille musamman daya kasance yana duka wani lokacin, toh da nayi tunanin ko aure zai zama maslaha agare shi musamman danaji kace kana ganin yanayin tashin sha'awarshi wani lokacin to inda matsalar take matar da zata aure shi din...!''

Duk shiru sukai na wani lokaci kowa da tunanin da yake sak'awa cikin ranshi, kafin alhaji Aminun ya kuma gyara zama yana cewa.

"Amma ka koma gidan su Fatima kuwa?''

"Eh wallahi na koma amma babu wani bayani wai tama koma wajan kanin mahaifinta dake zaune a kasar India harta koma makaranta.''

"kai Abu beyi kyauba wallahi kaga inda tana nan ai da duk ba'a yi wannan doguwar wahalar ba, toh amman duk da haka zancigita kaima saika cigita, ammafa namiji za'a samu ba mace ba kamin Allah yasa asamu wadda zata aureshin a haka.''

"Toh shikenan insha Allahu nima zan cigita bari na koma kafin ya tashi daga bacci ya hargitsa d'akin nasa.''

Har ya koma gidan bacci Haidar yake yi, lokacin har anyi sallar magriba yaje yayi shima, sai da ya sai mishi fura mai kyau da dad'i a hanyarsa da dawowa sannan ya shiga d'akinshi. Ido ya zuba mishi ganin yanda yake ta mutsu-mutsu amma yaki bud'e idanunshi, dafashi yayi yana cewa.

"Haidar...! Kai haidar..!!'' D'agoshi yayi yana kallon fuskarshi kafin yace. 

''Yanzu haka fitsari zaka yi kaketa wannan mutsu-mutsun...,Yauwa ai dama na sani.'' 

Maganar shi ya yanke lokacin da yaga fitsari na biyo kafar wandon Haidar d'in dake kwance. Wasu irin hawaye ne yaji sun zubo mishi kamin kuka me sauti ya biyo baya yana furta.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post