[Book] Sabon Al'amari Complete by Bilkisa Ibrahim

Sabon Al'amari

Title: Sabon Al'amari

Author: Bilkisu Ibrahim

Category: Fiction

Doc Size: 457KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2017

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya "Bilkisa Ibrahim" mai suna "Sabon Al'amari" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Da gudu suka shigo ďakin kowa yana maida numfashi, mama dake zaune abakin gado tana ninke kaya tadaka musu tsawa, kai wai lafiyarku!!!!.???

     Bathroom suka shige batareda sunbawa mama amsaba.

   Mama ta maida kallonta ga 'kofa da ake 'ko'karin buďewa, tasan tabbas wani suka takalo daga cikin yayyensu, ilai kuwa hasashen mama gsky ne, wani 'kya'ky'kyawan saurayi ba'ki yashigo yana hura hanci, hannunsa ri'ke da belt .

   Ganin mama a tsaye yasa yay 'kasa da kai, ya rissina yana gaisheta, mama ta amsa tana kauda kai gefe, tashi yayi ya fice dan bazai iya cigaba da ďaukar matakin dayay niyyaba.

    Bayan kamar minti goma da fitarsa mama ta ce, "marasa kunya saiku fito!!.

   Saida suka ďan le'ko suka tabbatar yafita sannan suka fito kowa fuskarsa tana nuna alamun tsoro.

   Mama ta hararesu mikuka yimasa?? Marasa kunya!.

   Matasan 'yammatan biyu masu matu'kar kama da juna suka shiga kallon kallo, kowa bayaso yafaďi laifin dasukayi, mama tasake daka musu tsawa, wai badaku nakeyi bane??,.

   Cikin rawar baki Nurr ta ce, "mama dama yayane yasakamu gyaran...........saikuma tayi shiru tana sosa 'keya,, mama ta hararesu kunsan ALLAH zan aika akirashi yazo yaci ubanku.

   Da sauri deena ta ce, "gyaran ďaki yasakamu shine muka zauna duba wasu takardu daya ajiye, harya dawo bamu gyaraba, shine yabiyomu zai zanemu.

   Mama taja tsaki kudai kuka sani mara mutunci, kunfison kullum ayita dukanku kamar jakuna ko??, kune zakuyita shan wahala abanza, ni ku fice kubani waje masu kunnen 'kashi kawai.

     🚶sum sum suka fice kamar munafukai, afalo sai la6e2 sukeyi, dan suna tsoron yin gamo dashi.

   Saif dake cin abinci afalon ya bushe da dariyar mugunta harda buga kai da kujera, ya ce, "matsoratan banza, aii wlhy dama na ri'ke masa ku........Nurr ta harareshi to ďan haďi basai ka ri'kemuba yanzuma aii baka makaraba mtsoooow.

   Saif ya harareta kwacika bakifa yanzu tunda kunga ya koma ďaki, wlhy yau daba ďakin mama kukajeba da kun daku, dan nasan da mami ce da badaku zatayi........, deena taja tsaki yanzuma kaje ka sanar dashi mun fito mana.

   A'a mikukeci nabaka na zuba, aii wlhy nasan ba 'kyaleku yayi ba............kafin yarufe baki wani saurayi mai tsananin kama dana ďazu yashigo falon, 'yammatan suka sake ranta ana kare zasu afka ďakin mama.

   Da sauri saurayin ya ce, "ku kuma lafiyarku????, sukaja birki danjin ba muryar na ďazu bane, Saif yasake tun tsurewa da dariyar mugunta, cikin dariya ya ce, "yaya Fahad sun zatafa yaya Mahmud ne, matsorata kawai.

    Yaya Fahad yazauna yana faďin hala laifi sukai masa?, eh mana laifi sukai masa yabiyosu zai lakaďa suka sha a ďakin mama, shine dasukaga ya koma ďaki suka fito zasuyi mana salo.

   Yaya fahad ya maida kallonsa ga matasan 'yammatan yana murmushi, ya ce, "autara's bakwajin magana ko kaďan wlhy, aii yaya Mahamud ďinne maganinku, saikuzo ku zauna tunda baya nan, danna haďu dashi a gate zai fita.

   Nurr ta ce, "dan ALLAH yaya Fahad da gsk kakeyi??, kar sai mun zauna ya shigo fa."

  Yaya Fahad yay dariya to kuce yau atsaye zaku wuni kenan?..........mami dake sakkowa daga saman daddy ta kalli su Nurr dake tsaye cirko2👯 kamar kaji, ta ce, "kukuma lafiya???.

    Saiff yashiga zayyano mata yanda akayi,, mami ta hararesu wlhy tun kafin na aika akira mishi ku wuce ku gyara masa ďakin, inkuwa ba hakaba zaku gane kurenku, aini mama bata 'kyauta miniba dabata bari ya jibgekuba, marasa kunya kawai, oya kuwuce mana tafaďa tana nuna musu hanyar fita...

    Jiki a sanyaye suka fice dan sunsan ba 'karamin aikin mami bane taďaukesu da kanta takai masa.

   Awaje suka tsaya suna kallon kalo, Nurr ta ce, "deena mun shiga uku wlhy tsoro nakeji, kinsan dai dukan yaya Mahamud sarai babu sau'ki, ta 'kare maganar da zubo da hawaye.

    Deena takamo hannunta kinga muje kafin yadawo mu gyara masa tunda yaya Fahad ya ce, "baya nan.

   ďakin suka nufa zuciyarsu tana dukan uku uku dan tsoro😜.................

...........Atare suka shiga ďakin gsky ďakin ya haďu, tamkar da mace aciki, Nurr ta ce, "mu raba aikin wani yayi bedroom wani yayi falo, yanda zamuyi mu gama da wuri.

    Deena ta ce, "to jekiyi bedroom ďin, amma dan ALLAH karki zauna wasa, dan nasan kin iya shiririta, Nurr ta ce, "matsalarkice kuma wannan, tafaďa tana shiga cikin bedroom ďin daya 'kawatu da 'kyawu.

               Dagewa sukayi suna aiki cikin hanzari, burinsu suyi sugama kafin mai ďakin ya dawo, sunkuwa yi saurin gamawa, Nurr ce kawai bata 'karasa wanke bayiba, deena tashiga tana tayata dansu gama da wuri.

    Batareda sun saniba ya dawo, 'kofar yasakama key yadawo saman kujera ya zauna, 'kafa ya ďora ďaya kan ďaya yana jiran fitowarsu.

   Cikin hanzari suka fito Nurr ta kwalla 'kara dan ganin wanda suke tsoron haďuwa dashi a zaune, da gudu suka isa bakin 'kofar da zummar guduwa, amma sai sukaji 'kofar gam da key, yadaka musu tsawa data sakasu durkushewa awajen suna rawar jiki, tamkar wanďanda suke cikin dusar 'kan'kara.

   Belt ďin jikin wandonsa yaxare yanufi inda suke, tuni suka 'kara tsurewa, Nurr uwar 'yan tsoro harta fara fitsari awando, tuni hawaye sun wanke mata kumatu, dama akwaita da tsoron duka, saikuma rashin kunya fal cikinta, deena tafi Nurr dauriya sosai.

   Ya zazzare musu manyan idanunsa, cikin 'karaji ya ce, "ku bakwajin magana ko,, kun manta da gargaďin danayi muku wancan weekend ďin ko??, kun raina kowa agidan nan, saboda kunnen 'kashi.

  Nurr zata fara rantse2 ya zura mata ďaya a baya, ta kwala wani uban ihu kamar wadda aka kashe, itama deena aka bata ďaya, saida yay musu uku2 sanana yabarsu, zuwa lokacin sun cika gidan da ihu.

   Yaya fahad yazo yana bashi ha'kuri sannan yabuďe 'kofar yafito yana huci.  ALLAH sarki yaya Fahad sarkin tausayi, shigowa yayi yatadasu yana lallashi, yakamo hannunsu zuwa babban falon kowa yana kwasar kuka, suna shiga sukayi arangama dashi a babban falo zaune, da gudu suka shiga ďakin mama, tabisu da kallo rai a 6ace, baki kawai ta cije tafito falon.

    Cikin faďa ta ce, "kai yanzu nan saida kadoki yarannan akan abinda bai taka kara ya karyaba  ko??.

    Yay 'kasa da kai, ALLAH mama yaran nan basa jin magana kwata2, yanzu idan na 'kyalesu gobe zasu yimin abinda yafi haka, tunda kunnen 'kashi garesu.

   Mama ta ce, "ai ka 'kyauta, nakuma gode,, ayi ha'ku yafaďa yana 'kara rissinar da kai 'kasa, mami tafito daga ďaki tana faďin aini yaymin dai2 wlhy, suba sun raina kowaba agidannan??, gobema idan suka 'kara yaymusu wanda yafi haka.

    Mama ta ce, "ALLAH mami kibar zugashi, dan bazan yarda ya illata min yara abanzaba.

   Babu wani illatawa mama, kema kinsan halinsu sarai, inda basuyi masa laifinba ai bazai dakesu ba ko.

   Mama tajuya cikin đaki tana faďin ai dama mami kekike goya masa baya.

   Babu wani goya baya anan, gadai gsky sai a'kita, saboda shi babba an maidashi juji, kuma ba'kya son laifinsu deena agidan nan.

   Ya Mahmud ya ce, "ALLAH mami yaran nan basuda mutunci, kuma ita mama bataso a hukuntasu idan sunyi laifi, karka damu My son daga yanzu suka 'kara yimaka laifi ka zanesu karka ďaga musu 'kafa.

    Mama tana jinsu tayi shiru dan tasan harda halin yaran, yaya Mahmud yanada zafi sosai amma bashida saurin duka, dan bakomai yake saka musu bakiba saboda bashida yawan magana, idan kaga yayi duka to an kaisa ma'kura kenan.

ASALIN LABARIN

    Sardauna family shine sunan da'ake kiran ahalin dangin.

    Dangine na 'yan boko kuma 'yan kasuwa, dan 'kalilanne acikinsu suke aikin gwamnati, kan mutanan family ďin  ahaďe yake babu wani bare daya isa yaji sirrinsu, ko auratayyama atsaka ninsu sukeyi, kusan family ďin duk auren dangine.

   Basa yarda ďansu ko 'yarsu ya auri bare saidai idan ALLAH ne ya 'kaddara hakan, ko kuma zaka ajiye matar data wuce ďaya, tofa wannan kanada damar auren bare idan kaso.

     Awannan familyne aka samar da Alhji Abdul'malik, wanda ďane na goma awaje Alhaji mutallaf Sardauna.

    Alh Abdul'malik yanada mata biyu da yara tara.

   Hajiya suwaiba itace uwar gidansa, suna kiranta da mama, itama tafito daga tsatson Sardauna family, dan ďiyace ga 'kanin Alh mutallaf, yaranta shidda dashi, Mahmud shine ďanta na fari, dan batama faďar sunansa, akwai kunya tsakaninta dashi, babu wata sha'kuwa mai yawa tsakaninsu, ko hira bata shiga tsaka ninsu saidai idan ya zama dole, bata shiga harkarsa ko kaďan, bama tafiya sakashi a al'amurantaba, wannan dalilin yasa yafi sha'kuwa da daddyn sa Alh Abdul'malik, dakuma mami.{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post