[Book] Yar Kwalliya Complete Hausa Novel by Husba Ahfama

Yar Kwalliya

Title: Yar Kwalliya

Author: Husba Ahfama

Category: Love Story

Doc Size: 235KB

Doc Type: TXT

Pub Year: 2019

Description: Sauke cikakken littafin marubuciya "Husba Ahfama" mai suna "Yar Kwalliya" complete hausa novel muka kawo muku. A text document, pdf, docx ko epub. Za ku iya daukarsa.

Book Teaser: Wata yarin yace 'yar shekara 15 kafa fururu komai babu fuska kuma tasha Jan baki da hoda harda gazal ta fallo da.

Gudu kanta daukeda tulo tadebo ruwa a guje ta fada gida Tana shiga ta saki tulun yafadi ya fashe.

Nidai gaskiya bazan yar daba hikenan ni banda kata bus hine fa ya bini har inda zan debo ruwafa inna  yana cemin.

 *YAR* *KWALLIYA* kafa ba mai fuska tasha ado hine nakamahi da danbe na fasa mihi baki hine dan bahida kunya ya biyoni gida.

Yasin bazan yarda ba inna kalli yanda bakina yake zubar jini inna Abu muguwace wlh.

Kayi hakuri kaji kaima da naka ina ruwanka da tsokanar ta kuma kasani sarai bazata barkaba.

Au abinda zaki ce kenan to shi kenan zan turo me rama min.

Kayi hakuri mana kai baka jin hakurine kna kotsayawa beyiba yatafi.

Inna ki barhi ki barhi nace kaje ka kawo bindiga karhe kenan. 

Yanzu Abu Wannan rayuwar kika zaba to shikenan zandena tsare miki wlh tinda ke bakida hakuri yanzu Wannan gabjejen kato kika kama da fada.

Inna hinefa ya nemi tso kanata fa.

Yanzu ruwan da kika debo ma gashi kin fasa tulon kaini inna ina zansa kaina.

Inna Wannan fa laifin tulun kine ina ruwanhi dani nan naso na ajiye hi hine ya fadi ya fahe sai hakuri.

Kamarya sai hakuri Abu girkifa zan Dora yanzu ya kikiso ayi.

To ni kome ma  za ayi ayi tuludai yafahe nikuma na gaji bazan iya komawaba.

Kin isa komawa kamar kinyi kin gama ga wani tulun can jeki dauka kidebo wani ruwan.

Kai inna kinemo wani ya debo kinga janbaki da hudana ya kare sonake na zagaya baya na siyo.

I dan har baki debo ruwan nan ba ba inda zaki Abu kin jini da kyau.

hikenan zan debo.

   Abu ta dauki tulun tatafi. 

Rake yauwa bari naga.

 Maya finda ke daure a kugunta ta kwance ta Ciro Hamsin ta mika wa me rake.

Yabata rake da canji tana tafe tana sha harta karasa rafi.

       Yauwa wana kama wato jiya kika watsa min kasa kika gudu ko yanzu wana kama cewar Abu.

Ke Abu kinga diban ruwa aka turoni ba fada ba matsa na wuce cewar binta.

Ke binta me kike nufi ni wasa aka turoni kenan bari kiga wasa cewar Abu.

    Hannu tasa ta ture tulun dake kan binta yafadi kasa yafashe.

Yauwa kinga wasa nan nafasa banza ko kinada abinyi ne.

Kaiiii ni kika fasawa tulu wallahi kinyi karya saina rama Abu kome kike takama dashi kin tara kin samu ni binta saina gyara miki zama.

Binta na gama fada tasa kafa ta daki tulun Abu yafashe.

Nanfa Abu ta daka tsalle ta dire ta kamo wuyan Binta suka kama fada da kyar aka rabasu.

Aina fada miki Abu ni Binta nice dai dai ke saina gyara miki zama.

Tohi kenan idan baki gyara min zamaba nizan gyara miki kuma saikin biyani tuluna kona  daka ki a gurin nan wlh.

Allah ko Abu bazan biya ba kiyi abinda kika gadama koda me kika zo ni Binta na fiki.

Haka kikace ko to hikenan.

Kallon ta Abu take tana gyada kai da buga kafa.

Banga wanda ze fi karfinaba ni Abu wai saiwata banza bazara iskar damuna binta wlh kintarowa kanki aradu da ka.

Hannun ta Abu ta kama ta sakar mata cizo dagudu tabar wajan.

Binta tabi bayanta da gudu haka suka yanka cikin unguwa dagudu harzuwa gidansu Abu.

 Abu ta boye a bayan inna.

Inna ki matsa Wannan fadan ba naki bane kimiko min Abu na nuna mata abinda binta zata iya ni kika ciza dai ko cewar Binta.

Yar gidan marasa tsoro mekikeyi a bayana aina fada miki ni nadena bada hakuri kinga Binta gata nan zoki mata abinda kike so cewar inna.

Gadan gadan Binta tataho.

Kinga Binta tsaya Abu ina ruwan dana aikeki kidebo cewar inna.

Inna asara kika aika dankuwa ni Binta nice nan na fasa tulun *'YAR KWALLIYA* tafasa min nawa shine nima na rama wata tsiyarce cewar Binta.

Ahh babu bakomai kinyi daidai yanzudai kiyi hakuri Binta kibari idan tafito kuyita takare mutuwama tana tsoron idon ma haifi cewar inna.

Inna kenan kince haka ko to ina waje ba inda zanje kekuma Abu zaki fito kisameni hoda bawanka kidinga Wanka idan zakiyi kwalliya.

 Binta tajuya ta fita.

Inna ki matsa kibar ni da ita kina jin metake cemin.

Karya tayi Abu gaskiya tafada yau kwananki nawa rabonki da kwanka.

Inna batun wankan nan kibarhi aikyan kwalliya kayihi batateda wankaba gawani kamhin turare na musamman.

 Dayake tahi a  jikina gahi turaren babu a kasuwa me yafi raina shine zan tsaya  inta batawa kaina lokaci wajan yin kwanka.

Dalla rufemin baki kazamar banza kazamar hufi ina kyau Anan *HODA BA WANKA*.

Baki tabude ta gir_giza kai ta dunkule hannu.

 inna harda ke yasin duk wanda yasake ce min hoda ba wanka na dena raga mihi yasin cewar Abu.

Yanzu da kika dunkule hannu damben zakiyi dani nima cewar inna.

Jifa tayi da takalmin kafarta ta debo kayan Kwalliya ta zube a gabanta tadauki Wannan tashafa ta ajiye takalli kanta a madubi tayi dariya.

  Inna jiya da naje dan dali aka dinga tambaya waye yafesa turare nayi shiru tsabar kanhin turaren jikina hanci suka toshe.

Niko kayan nan ma bacanzasu zanyi ba Wanka kuwa nadena.

 Kaza kankida motsi afakaice suka zageki baki saniba ba abinda kikeyi sai bugawa kitemaka ki ajiye kayan kwalliya kiyi Wanka kekanki zakiji dadi.

Tab tab aaah waii saidai wata Abun badai niba wanka nida hi munyi hannun Riga inna kifara sabon lissafi daga nan harranar sallah nida Wanka.

Haka kikace to Allah yashigoda yayanki da malam su insun isa dake Sa saki kiyi tinda ni kin rainani dan Allah ji yanda kika cika mana gida da tsami cewar inna.

Kinji ko inna kinji irin kamhin turarena ko hakama wani saurayi yajiyo kamhin yace yana sona nace bana son hi ni fako inna har bana son fita dik inda nabi ansan nice saboda turturarena cewar Abu.

Waiyoo waiyoo tasa kafa tayi koli da kayan kwalliya.

 Inna ban fada mikiba yau ake cin kasuwar gangare natafi.

 Tayi fice warta.

Badan Allah yasa akwai sauran ruwa agidan nan ba da Abu ta gama dani cewar Inna.

Tafiya take a hankali tana tafiya tana yanga acewarta tafi kowa haduwa ga turaren jikinta yafi na kowa kanshi tana tafe tana cin gyada hannun takuma rikeda sandar rake ga wuwar danmara tasha a kugunta.

binda na labe tana kallon ta Abu nakara sowa inda Binta take Binta tariketa.

Wana kama yasin saina dagargaza bakinki zan kyaleki yanzu ina inna take balle kibuye a bayanta cewar Binta.

Yasin Binta kanki baya aiki kalli yanda kika rike min Riga a gaban mutane gasamari a gefe kalan ki zubarmin da mutunci a idonsu haba kidena abinda kuda zebiki.

Karsan kuda nice mangoro kobakijiba cewar Binta.

 Janyota tayi zata daka bashiri ta saketa tatoshe hanci.

Abu dagaskene abinda ake fada kenan Wannan warin daga ina lallai kinci sunan ki huda ba Wanka sammin raken mana.

{getButton} $icon={download} $text={Download Book}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post