Budurwa Ta Fasa Aure Bayan Ta Gano Wanda Zai Aureta Ya Yiwa Uwarta Ciki

Anyi Ciki

A kwanakin baya mun kawo muku labarin yadda wata budurwa ta kama uwarta da Saurayinta. Sai dai a wannan karon, abun ya girmama. 

Domin ita wannan budurwar ta gano wanda za a daura mata aure da shi a watan December mai karatowa ya samawa amarya tasa kani ta hanyar yiwa uwar da ta haifeta ciki.

Kamar yadda shafin Tsangayar mu ta samu labari. Budurwar ta gano hakan ne bayan da saurayin da mahaifiyar yarinyar suka yi kuskuren tura sako inda sakon saurayin nata ne ya fada cikin wayarta.

Duk da dai budurwar ta shedamini ta jima tana zargin irin alakar dake tsakanin Mahaifiyarta da manemin auren nata, tace bata taba tunanin alakar tasu har ta kai hakan ba.

'Duk duniya babu wanda na sanarwa wannan batun sai kai bayan nayi dogon nazari da tunanin wanene zai fadawa wannan labarin domin na samu sauki a zuciyarta sai ka fadomini". Ta bakin amaryar December data fasa. 

Wato kanaji ko, ranar da asirinsu zai tonu, kawai sai naji sako ya shigo mini, amma kamin na bude ta WhatsApp ne sai aka goge, sako ne daga wajen shi saurayin nawa. 

Saboda ko an goge sako ina iya karantarwa, tofa a nan ne naga abunda ya rubutawa mamanmu yana rokonta ta zubda cikin dake tare da ita tunda dai tasan bana Baban mu bane domin kada nan gaba abun ya bayyana. Inda yake ce mata yana tsoron kada abunda zata haifa yayi kama dashi. 

Ina karantarwa sai naga kamar dai kuskure nake, ba sunana ya ambata a rubutun nasa ba. Sai da nayi kusan mintuna 10 ina rike da wayar na kasa cewa komai.

Tabbas mamanmu tana da ciki zai kai watanni 6 yanzu haka. To amma sai nace domin na tabbatar bari nayi kokari ko zan ga sakonsa a wayar mahaifiyar mu. 

Amma kamin nan na tambayeshi wani sakon ya turo mini kuma ya goge sai yace gaisuwa ce amma yayi kuskure rubutu shi yasa ya goge.  Wayar mamanmu yanada wuya ka ganshi babu makulli tamkar wayar karamar yarinya. 

Amma kusan kwanaki 3 nayi ina bibiyan yadda zan bude wayar na gagara. 

A kuma duk tsawon kwanakin nan babu wanda yasan halin da nake ciki har shi saurayin nawa duk da baya gari ban nuna masa akwai wani matsala ba.

Bayan kwanaki 5 da faruwar al'amarin ne sai kawai mamanmu ta mika mini wayarta tace tana so na duba mata bata jin magana sosai idan an kirata. Tana mika mini sai makociyar mu ta shigo wajenta nan ne fa na samu damar da zan bincika wayar nan. 

Amma babu inda ban duba ba sam banga wani alamu sako daga wajen shi ba. Haka na duba WhatsApp dinta kaf babu. Babu kuma lambarsa a wayar ta. 

A haka na hakura na mika mata wayarta bayan na gama duba mata.

Cikin dare naji mahaifiyata tana magana a waya, na zaci da mahaifinmu take, domin nasan idan baya gari irin haka suna hira ta waya, amma da yamma cin yau bayan tayi waya dashi ta bani mun gaisa inda yace mini a daren nan suna hanyar shiga daji ne domin artabu da masu garkuwa da mutane. 

Wannan yasa nayi likimo ina son sani dawa mamammu take waya. 

Kawai kalmarta ta kusan karshe sai naji tana cewa baza ka tambayi amaryarka bake nan yau gata can a dakina ma take kwance. Da wannan ne ta yi sallama da shi da kashe wayar. Ashe wata waya daban ta saya take magana da shi bada wayar dake hannunta ba.

Sai dana tabbatar naga inda ta boye wayar. Na sake jan mayafina na rufa nayi kamar bacci nake. 

To wannan wayar itace dai ba daukota da ita kuma na nunawa mahaifiyata naji komai nasan kuma komai. Sai dai na mata alkawarin bazan fadawa mahaifina ba. Tare da sharadin zata zubda wannan cikin.

Shi kuma mai son auren nawa bayan komai ya bayyana na ce masa na fasa auren tsakanina dashi Allah Ya mana hisabi. Duk kokarin wani bayani da dukkaninsu biyu suka so su mini zuciya bata bari ma naji ta yadda hakan ya samo asali ba.

Sai dai abunda ya daure mini kai game da mahaifiyar mu shine irin yadda mahaifin mu yake kula da ita, mu biyu ne kadai ta haifa kuma dukkanin mu mata nice kuma babba.

Wannan labarin dai anan muka datsai shi domin yanada tsawo. Abun fata shine Allah Ya rabamu da bin son zuciya.

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post