Gwanja: NBC ta haramta sa wakokin "Warr" da "A Sosa" a Gidajen Rediyo da Talabijin a Najeriya

Gwanja da Nbc

Hukumar dake kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa NBC ta haramta sanya waƙar Ado Gwanja ma taken "WARR" da kuma daya wakar tasa mai taken "A Sosa" a gidajen Radiyo da Talabijin a faɗin ƙasar nan.

A cewar takardar sanarwar hukumar, wakokin na dauke da wasu kalamai ne wadanda su ka yi hannun riga da kyakkyawar al'adar malam Bahaushe.

Wakar Warr na dauke da kalmomi na rashin da'a da kuma tallanta shan giya da yi  mariya a bidiyon wakar, hakan yasa hukumar taga ya dace ta dakatar da saka wakar a gidajen rediyo da talabijin.

Irin kalaman rashin da'ar sun hadar da;

"Kafin a san mu ai mun ci kashin ubanmu, 

 "Za na zo, bari in shafa hoda, ko kin zo da ke da hodar ubanku zan ci,  wa...

"Kowa yace zai hana mu ubansa zai ci...{getButton} $text={TELEGRAM CHANNEL}{getButton} $text={WHATSAPP GROUP}{getButton} $text={HAUSAEDOWN TV}

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post