😠Ke Duniya! Wani Mahaifi Ya Yi Wa Yar Cikinsa Fyade Tana Barci

An Kamo Mai Laifi

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekaru 46 mai suna Olusegun Oluwole bisa zarginsa da keta mutuntakar ‘yarsa cikinsa ‘yar shekara 17 da aka sakaya sunanta.

Kamar yadda jaridar Punch ta wallafa, ta ce, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya kutsa cikin dakin diyar tasa ya yi mata fyade a lokacin da take barci.

Sai tuni rundunar yan sandan jihar ta ce kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin zuwa ga sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya, yayin da kuma aka garzaya da yarinyar asibiti don duba lafiyarta.

To, Allah shi kyauta inji 'yan taska.


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post