Mijinta na nemanta lokacin watan Azumi da Jinin al'ada, wata mata ta roki kotu ta raba aurensu

Shari'a Law

Wata mata mai suna Zainab Yunusa ta maka mijinta Garba a kotun Shari’a dake Magajin Gari a Kaduna inda ta bukaci ya sallameta (saketa) saboda yana nemanta da mu'amalar aure da ya ke a lokutan da basu dace ba.

Zainab ta bayyana cewa mijin nata yana nemanta a lokutan da ta ke yin al’ada sannan kuma hatta a cikin watan Ramadana baya raga mata wanda hakan kuma ya sabawa koyarwar addinin Musulunci.

Sannan tace yana hanata abinci kuma baya barin danginta suna kai mata ziyara, saboda haka ne take rokar kotun ta umurce shi ya sallameta, amma shi mijin nata ya karyata wannan korafin nata.

Yace karya take yi kuma kafin ta gudu daga gidansa ita da mahaifiyarta sun sayar masa da kayayyakinsa, wanda hakan yasa alakali yace tazo da mahaifiyarta a ranar 27 ga watan satumba domin a cigaba da sauraron wannan shari’ar.

Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post