[Series] Labarina Season 5, Episode 1 HD Video Download

Labarina Season 5, Episode 1

Sauke tare da kallon shirin nan mai dogon zango, wato Labarina, Season 5, Episode 1 wanda tashar Saira Movies ke kawo muku a kowanne karshen mako.

Shirin Labarina dai fasihin marubucin nan, Ibrahim Birniwa ne ya ke rubutashi, shi ko hazikin fitaccen daraktan nan, Aminu Saira ya ke bada umarnin shirin.

A season 1 zuwa na 4 mun ga yadda shirin na Labarina ya matukar sauya akala, daga kan soyayya Mahmud da Sumayya, barin gidan da Mahmud yayi.

Dawowarsa gida, badakalar Sumayya da Presdor, har zuwa rasuwar Mahmud da kuma batan Sumayya.

Kai a dai cikin haka, sai ga Baba Dan Audu ya yi tsudum ya fara sabuwar dirama a cikin shirin, da shi da yake warewa a shirin sai ya dawo kuma shi kejan ragamarsa.

Yanzu haka dai Baba Dan Audu sun aikata laifin garkuwa da mutane, an kuma yi nasarar damkesu, suna cikin gidan gyaran hali. To, a nan shirin na Labarina ya ci gaba.

Ina daukacin masoyan wannan shiri mai dogon zango? Ku kalli episode na 1 yanzu a tashar Youtube ta Saira Movies:

Ban son cikaku da surutu, fatan za ku kasance da wannan shafi (HausaeDown) mai albarka domin samun sabbin labarai game da shirin Labarina.

Ku cigaba da bibiyar wannan shafi namu, in kuma kuna da lokaci, ku yi mana sharhi.


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post