Tarihin Bello Turji Kachalla, Hatsabibin Dan Bindigar Zamfara

Bello Turji

Bello Turji Kachalla wanda aka fi sani da Turji wani jagoran yan ta'adda ne a Najeriya wanda ya addabi yankin Arewacin Najeriya Musamman jihohin Zamfara, Sokoto da Neja. 

An haifi Turji a karamar hukumar Shinkafi, Jihar Zamfara dake Arewacin Najeriya a shekarar 1994. 

Turji ya jagoranci wani gungun yan fashi a Zamfara wanda suka kai wani mummunan hari da yayi sanadiyar mutuwar sama da mutane 200 wanda galibin su mata ne da ƙananan yara (Kisan kiyashin Zamfara na 2022).

An haifi Muhammadu Bello wanda aka fi sani da Kacalla Turji a yankin Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke cikin Jihar Zamfara a yanzu.

Sai dai yankin na Shinkafi da kuma garuruwan Isa da Sabon Birni na Jihar Sokoto ƙasa guda ce a shekarun baya, abin da ke nufin babu haƙikƙa kan takamaimiyar jihar da aka haife shi, wato Sakkwato ko Zamfara.

A Shinkafi ya taso kuma a nan ne mahaifnsa ke zuwa da shi cin kasuwar dabbobi da sauransu kamar kowane Bafulatani.

Binciken da wani masani yayi ya nuna cewa shekarun Bello Turji sun kama daga 27 zuwa 35 a yanzu.

Shi ma mahaifin Turji Usman wanda aka fi sani da Mani na Marake ɗan asalin yankin ne, mai arzikin dabbobi, kuma mutum ne bawan Allah da ke da tarihi na zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

Mahaifyarsa Turji kuma, an fi saninta da yar Kagara – ta yankin Shinkafi, wadda ke da alaƙa da babban yaron Turji mai suna Danbokolo.

Uwa da uba da yan uwan Turji sun guje shi.

Bayanai sun nuna cewa baki ɗayan yan uwan Turji ba sa hulɗa da shi sakamakon sana’arsa ta fashi da makami.

Hakan ta sa mahaifinsa Mani na Marake ya yi hijira zuwa garin Kura na Jihar Kano, daga baya ya koma Jigawa. A watan Yulin 2021 an samu rahotanni cewa yan bindigar da ke biyayya ga Turji sun fantsama garuruwan yankin Shinkafi tare da sace mutane da yawa a matsayin martanin kama mahaifin nasa da aka yi.

Ya yi iya bakin ƙoƙarinsa (mahaifin Turji) don ya hana shi amma ya ƙi ji, saboda haka ya tashi daga Zamfara ya koma Kano.

Ita kuma Yar Kagara (mahaifiyar Turji) ba ma ta son a ambaci sunansa. Kuma mutanen da ke wurin sun shaide ta da cewa lamarin ya fi ƙarfinta da kuma mahaifinsa.

Yan uwansa na kusa da na nesa ba su da alaƙa da shi, ba sa karɓar duk wani abu da ya fito daga hannunsa na kuɗi ko kyauta saboda ba wanda ya yarda da abin da yake yi – idan ka cire Ɗanbakolo.

Turji Ya Yi Karatun Islamiyya

Bello Turji ya yi karatun Islmaiyya kuma yana da ilimi gargwado, amma ba ilimi mai zurfi ba kamar yadda mutane ke tunani.

Haka nan jagoran yan fashin ya yi karatun boko, inda bayanai suka nuna cewa ya kammala firamare.

Yaran Turji ba talakawa ba ne, akwai ya’yan manya

Manyan yaran da Turji ke jagoranta matasa ne masu shekaru irin nasa, waɗanda daga cikinsu akwai ‘ya’yan sarakuna da hakimai a yankin.

Wasu daga cikinsu waɗanda mafi yawansu abokansa ne da suka taso tare.

  1. Kacalla Ɓingyal – mutumin Kagara
  2. Ɓaleri – mutumin Sakai
  3. Alhaji Auta
  4. Bello Kagara
  5. Yalo Ɗanbokolo – ɗan uwan Turji na jini kuma babban yaronsa
  6. Malam Ila Manawa
  7. Yalo Emiya
  8. Abdullahi – mutumin Kagara
  9. Umaru Nagona – mutumin Kagara

“Misali, akwai Ila Manawa wanda mahaifinsa mai garin Manawa ne, yana cikin manyan yaran Turji.

Duk waɗannan yaran ba talakawa ba ne, suna da hali da duk abin da kake tunani, dukiya a wajensu ita ce shanu.

Kuma dukkansu suna ɗauke da makamai a yau.

Bai daɗe da zama ɗan fashi ba. Bello Turji bai daɗe da fara satar shanu da kuma kashe-kashen mutane ba.

Ko a lokacin da wannan rikici ya fara a Zamfara lokacin su Tsoho, wanda aka fi sani da Buharin Daji, Turji na ƙarami kuma bai shiga wannan aƙidar ba. Daga baya ya shige ta.

Shan giyar kusu Turji yayi wajen shiga harkokin, duk waɗanda ke yankin za su faɗa muku cewa lokacin da ake yi (a wancan lokacin) kasuwa kawai Turji yake zuwa.”

Batun Tubansa A Watan Agusta 2022

Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da cewa Bello Turji ya amince da sulhuntawa da gwamnati. Mataimakin Gwamnan Zamfara Hassan Nasiha ne ya tabbatar da hakan a Gusau, babban birnin jihar a ranar Lahadi.

Ya ce tubar da Bello Turji ya yi ta kawo zaman lafiya a Birnin Magaji, Shinkafi da Karamar Hukumar Zurmi.

Mataimakin Gwamna ya yi wannan jawabi a wurin taron da Ƙungiyar Ɗaliban Jami’ar Madina ‘yan Jihar Zamfara su ka shirya ranar Lahadi.


Leave Your Comment (0)
Recent Post Next Post